Faifai na 3 : Tanadi (HA-3)
A lokacin hukunci na rigyawa, Allah ya tanada wata hanya ta kubuta ga dukkan wadanda suka gaskata. Bayan wadansu shekaru, a cikin gwajin da Allah ya yi da Ibrahim, akwai hoto mai daukar hankali da aka bayar na madadi da zai zo a nan gaba wanda zai bayar da rayuwarsa domin mutanen duniya.