Faifai na 4: Kubutarwa (HA-4)
Yayin da Allah ya fitar da mutanensa daga bauta, ya kwatanta cewa shi kadai ne Allah. A lokacin annoba ta goma, hanya dayan nan ta samun kubuta daga mutuwa tana nuni ne ga wata kubutarwa ta duniyar da ke cikin kangin zunubi da mutuwa da za ta zo a gaba.